Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: Barikin sojojin kasashen hadin gwuiwa ya kone


Kasar Kamaru
Kasar Kamaru

Barikin sojojin kasashe da suka yi karo-karo na hadin gwuiwa daga yankin Chadi dake Mora saboda yakar Boko Haram ya kone

Bangaren da ake ajiye manya manyan makamai da sauran kayan yaki shi ne ya fi konewa.

Gobarar ta sa al'ummar garin na Mora dake yankin duk sun fice daga gidajensu domin fitar da kawunansu suka haura kan dutsen da ya kewaye garinsu. Mutanen garin na tsammanin maharan Boko Haram ne suka kawo masu farmaki.

Mazauna garin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe dayan dare yayinda suka dinga jin fashewar bamabamai.

Lamarin ya firgita mtanen garin. Da suka san dalilin karar da suka ji sai suka fara komawa gidajensu.

Kawo yanzu babu labarin salwantar rai ko daya ko kuma jikatar wasu. To saidai ministan tsaron kasar Kamaru yace za'a gudanar da bincike domin a tabbatar da sanadiyar gobarar domin ana kyautata zaton akwai lauje cikin nadi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG