Wadannan dalibai 14, masu shekaru 13 zuwa 16, ana zarginsu da fyade, dillancin karuwai da kuma shan kwayoyi.
Bayan korafe-korafen iyaye da suka gano ‘ya’yansu suna dauke da dabi'un da ba su dace ba. An gano munanar ayyukansu din bayan rashin cika alkawari a tsakaninsu
Wasu dalibai maza sun bukaci lalata da kawayen karatunsu mata biyu kamar yadda suka saba. Kuma suka yi bidiyo suka yada a kafafen sada zumunta. Anyi haka ne bayan alkawarin bai wa kowace daga cikin matan jaka arba'in (40 000 F) na kudin CFA.
Rashin cika wannan alkawarin ne yasa yaran mantan suka kai kara wajen babban mai kula da su. Bayan bincike na cikin gida, shugaban makarantar ya kira taron majalisar ladabtarwa ta musamman.
Daga baya ne ya daukaka kara gurin alkalin da ya ba da umarni a zurfafa bincike. Wanda zai kai ga gane cewa, kungiya ce musamman take kafe don wadannan aika aika a cikin makarantu.
Musa Ousseini, shugaban kungiyar farar hula kuma mai kula da tarbiyar matasa yace lamarin abun mamaki ne kuma dole a tashi tsaye a dakile wannan dabi’o’I na batsa.
Binciken kuma ya baiwa wasu daga cikin daliban damar yin cikakken bayani. Sun bayyana cewa sun kasance karƙashin rinjayar wasu manya, wadanda suke shugabantar wannan kungiyar dillancin.
A cewar mai gabatar da kara, binciken da ake ci gaba da gudanarwa, zai ba da damar cafke daukacin shugabannin kungiyar da mabiyansu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: