Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Da Shirin Samar Da Ruga Ya Fuskanta a Najeriya


Gwamnatin Najeriya ta shafe shekaru tana neman hanyar warware rikicin dake tsakanin manoma da makiyaya game da wuraren kiwo, rikicin da ya lakume rayukan dubban mutane.

Wannan rikicin ya fi shafar yankin tsakiyar kasar da ya dade yana fama da rikice-rikice, amma kwanan nan gwamnati ta bullo da wani shiri na samar wa makiyaya wurin kiwo, da nufin kawo karshen rikice-rikicen. Amma wannan shiri na gwamnati, da aka ke kira RUGA yana fuskantar kalubale.

Rikici tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ya samo asali ne tun shekaru da yawa da suka gabata. Karin yawan jama'a, birni da kuma kwararowar hamada, Wanda ke haifar da karuwar canjin yanayi sun Kara dagula rikici.

Fiye da mutane 3,600 ne suka rasa rayukansu a wannan rikicin akan filayen kiwo, tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018. Sannan duban mutane suka rasa matsugunansu.

Gwamnati ta ce kafa wuraren kiwon shanun, ko Ruga ga makiyaya zai magance matsalar.

"Garba Abari, babban daraktan hukumar wayar da al’umma na kasa, ya ce, Abin da aka yi niyyar yi shi ne kawai a samo wata hanya ta takaita rikicin manoma da makiyaya."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG