Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KALLABI: Hira Da Hauwa Ahmed PT2-Darasi Daga Takarar KamalaPt1-Agusta, 25, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Shirin Kallabi na wannan makon ya kunshi kashi na biyu na tattauna da Hajiya Hauwa Ahmed, shugabar kungiyar mata zalla a jihar Kano, waddda a yau ta bayyana yadda suka sami jarin fara gudanar da shirin a daidaita sawu na mata.

Shirin ya kuma yi nazarin darasin da mata a kasashen Afrika za su iya koya daga takarar Shugaban kasar Amurka da Kamala Harris ta tsaya. Bakin da shirin ya gayyata domin nazarin wannan mukalar su ne Madam Helen Bako a California inda Kamala Harris ta fito, da kuma Malama Hafsatu Yakubu da ke zaune a Chicago inda jam'iyar Democrat ta tsaida Kamala a matsayin 'yar takara a yayin babban taronta na kasa.

Saurari cikakken shirin:

Hira Da Hauwa Ahmed PT2-Darasi Daga Takarar KamalaPt1
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:39 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG