Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KALLABI-EP010-Batutuwa- Matsayin Mata Kan Gwamnatin Buhari Da Fatarsu Ga Ta Tinubu- Tunawa Da Tina Turner-05-28-2023


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Shirin Kallabi na wannan makon ya maida hankali kan batun shirin mika mulki da rantsar da sabon Shugaban kasa a Najeriya da ya dauki hankalin kasashen duniya, inda tuni babban birnin Tarayya Abuja ya cika ya batse da baki daga ko’ina a duniya maza da mata.

Sai dai banda zuwa runfunan zabe domin kada kuri’a, da rantsar da zababbun shugabanni, i zuwa yanzu, mata basu kai ga samun tsayawa takara da lashe zabe da ya wuce na kananan hukumomi da majalisun tarayya kalilan ba. duk da haka, bai sa su yi kasa a guiwa ba, sabili da hankoron samun gwamnatin da zata kaisu ga cimma burinsu.

Yaya mata suka dauki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari Mai barin gado? kuma menene fatarsu ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da zata karbi mulki gobe? amsoshin da shirin kallabi ya nema ke nan wannan makon.

Saurari cikakken shirin:

KALLABI-EP010- Matsayin Mata Kan Gwamnatin Buhari Da Fatarsu Ga Ta Tinubu
please wait

No media source currently available

0:00 0:25:13 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG