Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Fusata Akan Cewa Rasha Nada Bayanan Sirri A Kansa


Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado

Zababben shugaban Amurka Donald Trump a fusace ya bayyana fushin sa akan bayanin rahoton da aka tattara na cewa wai kasar Rasha zata yi anfani dashi.

A cikin shafin sa na Tweeter wanda ya bayyana rahoton a matsayin mara makama balle tushe, haka kuma ya karyata wannan batun a taron manema labarai na farko da yayi a jiya Laraba, tun lokacin da aka zabe shi.

Trump yace wannan bayani abin kunya ne, har a bar irin wannan bayani ya fito sarari. Yace yaga bayanin, kuma ya karanta, amma duk labarin karya ne, yace sam wannan bai faru ba.

Rahotanni dai daga kafofin yada labarai sun bayyana cewa jami’an daga ma’aikatan tattara bayanan sirri na nan Amurka, a cikin rahoton da suka tattara sunyi zargin cewa shugabannin tawagar kamfen na Trump sun hada baki da jamai’an tsaron kasar Rasha, haka kuma sun tattauna akan batun dabi’o’in shi Trump na alfasha.

Sai dai babban lauyan zababben shugaban Michael Cohen ya fada wa manema labarai cewa wannan zargin dake cikin wannan rahoton ba kome cikin sa illa karya da kuma yunkuri zubar da kiman shugaba Trump.

Shima a nasa jawabin, mai magana da yawun shugaban na Rasha wato Dmitry Peskov ya fada jiya Laraba cewa wannan labarin ana yayata shi ne da niyyar kawo wa dangankatar Rasha da Amurka cikas.

Yace ba gaskiya ba ne Rasha bata da ko wani bayani ko rahoto na batanci game da Trump. Yace wannan rahoto sam baiyi dai-dai da abinda yake zahiri ba ne kuma ba kome cikin sa illa zuki ta mallaki.

XS
SM
MD
LG