Shugabannin nahiyar Afirka na dab da bukatar shugaban Amurka Donald Trump ya fito bainar jama’a ya nemi afuwa kan kalaman batanci da akace yayi kan nahiyar Afirka da bakin haure, amma sai suka canza shawara a cewar wani rahoto.
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta rubuta martaninta ga shugaban a taron kolin da ta gudanar cikin wannan makon.
Martanin da aka rubuta na gargadin cewa kalamun Trump na batanci da nuna kalibanci, ya saka dangantakar Amurka da kasashen Afirka cikin hadari.
Ta ce shugabannin Afirka sunyi mamaki ga kalamun da ake ce Trump yayi, “abin bakin ciki ne da mamaki kan kaskantar da mutanen da suka fito daga Afirka da ma wadanda ba farar fata ba da gwamnatin Trump ke yi.”
Amma sai kungiyar AU ta yanke shawarar kin fitar da wasikar. Tana mai nuni ga wasikar da Trump ya rubuta ranar 25 ga watan Janairu, wadda cikinta ne Trump yace yana matukar ganin mutuncin Afirka, ya kuma bayyana cewa sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson zai kara kai ziyara Afirka a watan Maris.
Haka kuma Trump ya gana da shguaban kasar Rwanda Paul Kagame a gefen taron kolin tattalin arzikin kasashen duniya a makon da ya gabata.
Yanzu haka dai Kagame shine shugaban kungiyar AU. Ya kuma ce ya kamata AU ta sami hanyar yadda zata yi mu’amala da Trump.
Facebook Forum