A karshen wani taro da suka gudanar karshen mako a birnin Lagos, kungiyar Injiniyoyin tace wannan hanyar itace mafita wajen kulawa da hanyoyin kasar da suka lalace, haka kuma idan har gwamnati na son gudanar da aiyukanta kamar yadda ya kamata da kuma yadda ake gudanar da su a sauran kasashe duniya a bullo da tashoshin da niyar kula da su.
Gwamnatin Najeriya tace tana son bullowa da shingayen biyan kudi ko tashoshi a manyan hanyoyi, sai dai ‘yan Majalisa sun nuna rashin amincewarsu. Shugaban kungiyar Injinoyoyi reshen jihar Neja, Injiniya Usman Lafai, yace matsalar da ake fuskanta a Najeriya itace babu wani shiri da ake yi na gyaran hanyoyi da zarar an gina hanya shike nan.
Kasashen da suka ci gaba dai na gina ire-iren wadannan tashoshi ko shingaye akan manyan hanyoyinsu domin samar da kudin shiga wajen gina hanyoyi da kuma gyaransu.
Sai dai a bangaren direbobin manyan mantoci da ko yaushe ake zargin cewa sune ke taimakawa wajen lalata manyan hanyoyi a Najeriya. kamar yadda ‘daya daga cikin direbobin tankokin mai ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibrin, suna bukatar gwamnatin tarayya da ta gudanar da gyara kasancewar yawancin manyan hanyoyi a kasar sun lalace.
Yanzu haka dai Najeriya na da hanyoyi masu tsawon kilomita Dubu 35 karkashin gwamnatin tarayya, kuma duk da cewa an kashe musu zunzurutun kudi har fiye da Naira Tiriliyan 1.5 daga shekarar 1999 zuwa 2015, amma har yanzu hanyoyin na da wahalar bi.
Domin karin bayani.