Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaduna Tana Shiri Ta Kaucewa Illar Ambaliyar Ruwa


Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwan da aka yi harsashe, zata shafi kananan hukumomin Kaduna irin su Kaduna da Arewa da Kaduna ta Kudu, Kubau, Kauru, Zaria,Chikun, da Soba da dai wasu.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta soma ilimantar da jama'a tare da fadakar dasu, musamman wadanda suke zaune kusa da bakin tafki, ko rafuka ko kuma babban rafin River Kaduna.

Hukumar ta fara haduwa da dagatai da hakimai domin fadakar dasu da zummmar samun goyon bayansu saboda su ma su yi hobasa wurin fadakar da jama'arsu.

Akwai kuma tanadin ko ta kwana da hukumar tayi.An horas da 'yan kwana kwana akan abubuwan da zasu yi da zara an samu almar ambaliyar ruwa a wani wuri.

Hukumar ta kira duk hukumomin dake kula da bada agajin gaggawa dake hukumomin jihar ashirin da uku. An tattauna da duk masu ruwa da tsaki a kan lamarin.

Kawo yanzu an soma samun ambaliyar ruwa a wasu wurare a kananan hukumomin Zaria da Kauru. Saboda haka ana rokon duk wadanda gidajensu ke bakin ruwa su tashi

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG