Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin da Ya Fado da Gangan Matukin Ya Sakoshi Kasa


Mahukuntan Faransa da suka bada sakamakon bincikensu akan jirgin da ya fado
Mahukuntan Faransa da suka bada sakamakon bincikensu akan jirgin da ya fado

Mahukuntaan kasar Faransa sun sanar cewa matukin jirgin ya sakoshi kasa

Hukumomin kasar Faransa sun ce daya matukin jirgin saman sufuri na Germanwings da ya gamu da hadari, ya karkatar da jirgin ne da gangan ya rafka shi kan tsaunukan kasar Faransa ranar Talata, ya kashe fasinjoji 150 dake ciki.

Mai shigar da kara na Marseilles Brice Robin ne ya sanar da haka jiya Alhamis, a wata hira da manema labarai ta talabijin, da ya ba shugabannin duniya da wadanda suka saurareshi a duk fadin duniya mamaki.

Robin yace shaidar da aka samu daga muryoyin da aka nada ta nuna, matukin jirgin dan shekaru 27 Andreas Lubitz dan asalin kasar Jamus, ya kulle abokin aikinsa matukin jirgi a waje daga dakin matuka jirgin A-320, daga nan yace, bayanda Lubitz ya kulle kansa a cikin dakin, sai ya karkatar da akalar jirgin da gangan yasa shi subutowa yana gudun kilomita dari bakwai cikin sa’a daya na tsawon minti takwas kafin faduwarsa.

Yace bayanan da na’ura ta nada ya kuma nuna cewa, fasinjoji basu san jirgin yana subutowa ba sai yana dab da faduwarsa, lokacin da aka ji ihu a na’urar nadar bayanan.

Robin yace, bayanan da na’urar ta nada ya nuna cewa, matukin jirgin wanda mai yiwuwa ya fita domin yaje bandaki, yana ta buga kofar yana neman shiga, amma shiru kake ji. Robin yace abinda aka ji kawai bayan kofar dakin matuka jirgin shine numfashin Lubitz.

Yace lumfashin ba na wanda ya razana bane,lunfashi ne da kowane mai rai ya saba yi. Robin yace, binciken farko ya nuna, faduwar jirgin bata da nasaba da ta’addanci.

XS
SM
MD
LG