Yayin da yan uwa da jamian ke ta kokarin ganin sun san dalilin da ya kawo faduwar jirgin nan mai suna Germernwing kirar AirbusA320 da ya fadi a inda ake kira French Alps, kuma yayi dalilin mutuwar duka fasinjojin da ma’aikatan dake cikinsa su 150, kwaran sai wani mai bincike ya kara ruda mutane game da abinda ya faru.
Wani mai bincike da ba’a anbaci sunan sa ba ya shaidawa jaridar Newyork Times jiya Laraba cewa daya daga cikin matuka jirgin ne yabar wajen zaman sa kuma ya kasa komawa akan lokaci kafin jirgin ya fadi.
Daga bayanan da aka samu a cikin na’ura mai nade bayanai a inda jirgin ya fadi, mai binciken ya bayyana wa jaridar ta New York Times cewa an jiwo daya daga cikin matukan jirgin na kwankwasa kofar wurin matukin sannu a hankali amma ba’a amsa masa ba, abinda yasa ya banki kofar da karfi amma duk da haka bata bude ba, kuma ba amsa masa ba.
Mai binciken yace daga bayanan da naurar ta nada ana iya jin yadda direban ke kokarin fasa kofar, yace sai dai abin tambaya anan shine ko mene dalilin da yasa kofar taki budewa?
Yace abinda ake da tabbaci akai shine daya daga cikin direbobin jirgin shi kadai ne kuma bai budewa dan uwan nasa kofa ba.
Jiya dai shugabannin kasar Faransa, Jamus,da Spain sun hadu inda wannan jirgin ya fadi domin nuna alhinin su game da wannan hadarin.