A Amurka, ana ci gaba da jimamin rasuwar dan majalisar wakilai Elijah Cummings, wanda ya rasu a ranar Alhamis.
Ya rasu yana da shekara 68.
Cummings jigo ne a binciken da ake yi wanda ke duba yiwuwar tsige Shugaba Donald Trump.
A ranar Alhamis ofishinsa ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce dan majalisar wanda dan Democrat ne ya rasu, sanadiyyar “rashin lafiya da ya jima yana fama da ita.”
A karshen watan Satumba, Cummings ya fadawa jaridar Baltimore Sun cewa yana samun sauki bayan da ya je neman magani a asibiti, yana kuma shirin dawowa majalisar a Washington a wannan mako.
Cummings dan asalin birnin Baltimore ne a jihar Maryland, ya kuma rike mukamin shugaban kwamitin da ke kula da harkokin majalisar da na yin sauye-sauye a gwamnati – daya daga cikin kwamitoticn da ke binciken da ke duba yiwuwar tsige Shugaba Trump.