Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohi Goma sha Daya na Arewacin Najeriya na Fama da Kwararowar Fama


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Masana kan canjin yanayi sun sha ja kunnunwan gwamnatocin Najeriya cewa hamada na dada mamaye wasu sassan kasar

Jihohi goma sha daya a arewacin Najeriya sun koka da yadda hamada ke kwararowa tana mamaye wasu wurare.

Gwamnatocin jihohin da kwararowar hamada ta fi shafa sun nemi doki domin shawo kan baraznar da hamada keyi masu. Kwamishanonin ma'aikatun muhallai na jihohin sun gudanar da wani taro a jihar Neja domin jawo hankalin gwamnatin tarayya da ma na jihohhin da abun ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za'a dauki matakan magance kwararowar hamada.

Alhaji Muhammed Lugga kwamishanan muhalli na jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar kwamishanonin na jihohin goma sha daya ya bayyana manyan matsalolin dake addabarsu. Yace yadda suke aikin shi ne yadda shugaban kasa ya amince a yi. Karo na farko an basu kudi miliyan dari uku da suka yi anfani da shi wurin yin shuke-shuken itatuwa a cikin jihohin. Amma tun lokacin da suka shuka itatuwan a shekarar 2013 ba'a karesu da wayoyi ba domin kada tumaki su cinyesu kuma ba'a yi rijiyar butsatsin ruwa ba domin a dinga ba itatuwan ruwa. Yanzu itatuwan da yawa sun mutu.

Shi ma kwamishanan muhalli na jihar Borno Alhaji Hassan Mustapha yace kwararowar hamadan na son yin awongaba da gandun dajin tabkin Chadi wanda a da yana da yawan kilomita dubu ashirin da biyar amma yanzu ya saura dubu biyu da dari biyar kacal. Yace ban da haka manoma sun bar karkara sun dawo gari domin ba zasu iya yin noma ba.

Gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu ya yi bayanin irin matakan da suke dauka. Yace idan an shuka itace a wani kauye kamar a jihar Sokoto ba'a shaidawa mutumin kauyen ba to yana iya ya tunbukeshi. Yace "To amma idan da su muka yi to shi ne muka tattauna yanzu cewa ita gwamnatin tarayya wannan abun da tayi niyar yi ta kuma yi alkawarin zata bada biliyan goma a fara a wa'yan nan jihohi goma sha daya. Tun daga Sokoto har zuwa Borno to ya kamata a fara a cigaba. Lokacin da aka yi alkawarin na biliyan goma to an saki miliyan dari uku ne".

Manazartar harakar muhalli sun ce samarda makamashin gas domin anfanin yau da kullum ga iyali zai taimaka kwarai wajen rage saran itatuwan yin dafe-dafe wanda daya ne daga cikin dalilan kwararowar hamadar
XS
SM
MD
LG