Gwamnatin jihar Jigawa, ta gudanar da tarurruka a shiyoyi daban daban na jihar Jigawa tsawon kwanaki kuma aka kamala shi a Dutse babban birnin jihar inda masu ruwa da tsaki suka yi musayar ra’ayi kan matakan bi domin kara inganta hakokin koyo da koyarwa.
Mataimakin Gwamnan Jigawa Barister Ibrahim Hassan Hadeija, wanda ya rufe taron da ma’aikatar ilimi ta jihar ta shirya, ya ce akwai bukatar su kansu Malaman a karamasu ilimin koyarwa kuma a nemi Karin Malamai kamar yadda ya ce ana neman Malamai sama da 3,000.
Kwamishiniyar Ilimi, ta jihar Hajiya Rabi Ishaq, ta ce abubuwa da dama Gwamnati zata yi kuma akwai abubuwan da al’uma zasu iya yi, kamar horas da Malamai Gwamnati zata iya amma kamar gina makarantu gyaran da tallafi da sa kujeru duk jama’a zasu iya taimakawa.
Kimanin kashi 40 cikin 100, na fiye da Naira Biliyan 37, da Gwamnatin Jigawa ke Muradin kashewa a shekarar kudi mai zuwa zasu tafi ne ga bangaren ilimi in ji Gwamna Badaru Abubakar.