Hukumar tattara kudaden haraji a jihar Filato ta ce harajin da jama’a ke bayarwa ya taimaka wajen bunkasa ayyukan more rayuwa, musamman wajen samar da tsaro a jihar.
A hirarsa da Muryar Amurka, shugaban hukumar tattara kudaden haraji a jihar Filato, Dashe Arlat ya ce tsarin da gwamnatin tarayya ta bullo da shi na tattara kudaden shiga a asusu guda da samar da lambar biyan haraji wato TIN Number, hanyoyine da ake tantance jama’a da sanin sana’ar da suke yi don taimaka wa gwamnati da bayanan da za ta yi tsare-tsare da zasu inganta rayuwar al’umma.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyanawa Muryar Amurka ra'ayoyinsu game da wannan kudade na haraji da gwamnati take karba.
Ga rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Facebook Forum