Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Hakimin Tama Hade Da Wasu Yara Biyu A Jihar Bauchi


Bauchi
Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi na bayanin cewar wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kama wani hakimin kauye, hade da wasu mutane Biyu, wani mutum guda kuma ya rasa ransa a kauyukan Tulu da Tama dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Wani mutum da ya shaida faruwar lamarin yayiwa wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammad karin bayani, inda yace wasu ‘yan bindiga ne kimanin su Ashirin suka fara harbe harbe da missalin karfe ‘daya na dare.

A cewar mahaifin yaran biyu da aka sace, yace da farko sun kama matarsa da ‘dan sa Allah ya kubutar da su, sai 'yan bindigar suka sake komawa gidansa, inda suka ‘kara dauko wasu yara biyu. Yanzu haka dai yaran da mai girma hakimin Tama na hunnun ‘yan bindigar. Daga baya ‘yan bindigar sun bar lambar waya domin a tuntubesu.

Wannan yanayi da ake fama da shi na satar mutane don neman kudin fansa na ‘kara yawa a jihar Bauchi. A gefe guda kuma har yanzu babu wani bayani daga ‘yan sandan jihar Bauchi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG