Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan kasar Japan yace yanayin masana'antar nukiliya ta Fukushima yana kara tsananta


Firai Ministan kasar Japan Naoto Kan
Firai Ministan kasar Japan Naoto Kan

Firai Ministan kasar Japan ya bayyana damuwa dangane da yanayin masana'antar nukiliya ta Fukushima

PM kasar Japan Naoto Kan yace yanayin da ake ciki a masana’antar nukiliya ta Fukushima ya tsananta ainun, yayinda sababbin rahotanni ke nuni da cewa, daya daga cikin tukwanen tashar ta lalace, makonni biyu bayan girgizar kasa da kuma kazamar ambaliyar ruwa ta tsunami. A wani jawabi da yayi ga kasa ta tashar talabijin, Mr. Kan yace tilas ne kasar tayi zaman tsaro kasancewa ana kyautata zaton yoyon da tukunyar ke yi zai ci gaba da karuwa. PM ya godewa ma’aikatan kwana-kwana da yace sun sadaukar da rayukansu a yunkurin sanyaya tukwanen ma’aikatar nukiliyar. Jiya jumm’a kuma babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi wata sanarwar inda ya bayyana goyon bayan kiran da ake yi na ayyana wani tsarin daukar matakin gaggawa na kasa da kasa da kuma tabbatar da lafiyar makamashin nukiliya

XS
SM
MD
LG