Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bada shawarar a yi kwaskwarima ga tsarin mulki ta yadda majalisun dokokin tarayya zasu zama na wucin gadi.Ta wan nan hanya inji janar Babangid gwamnati zata rage kashe kudi da take cewa bata dasu ahalin yanzu.
Haka kuma Janar Babangida yayi magana kan wasu hanyoyin rage ayyuka da gwamnatin tarayya dake gudanar wa yanzu.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a hira da yayi da sashen Hausa na Muriyar Amurka.
Saurari: