Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janal Babangida Kan Maganar Dage Zabe


Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya janar Babangida yace majalisar kasa ba zata yiwa hukumar zabe katsalandan ba, a cikin hira da yayi da babban editan Dandalin VOA Ibrahim Alfa Ahmed.

Janar Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya, yace lokacin da suke gudanar da taron kasa hukumar zabe mai zaman kanta INEC a takaice tana zaman kanta saboda da haka ba zasu iya gaya mata abun da zata yi ba sai dai su bada shawara bisa ga yadda doka ta tanada.

Tsarin mulkin kasa ya baywa hukumar ikon ta shirya yadda zata yi zabe, saboda da haka ba daidai ba ne su gaya mata abun da zata yi.

Shugaban hukumar zabe ya fadawa majalisar kasa duk abubuwan da suka yi, harma Janaral Babangida yace sun yi kokari. Amma akan matsalolin da suka taso sun umurci shugaban hukumar da ya koma yayi magana akai, daga baya ya dawo gaban taron ya bayyana masu. Janaral Babangida yace duk abun da ya fada masu basu da damar hana shi gudanar da zabe.

Dangane da barazanar da wasu magoya bayan 'yan takaran APC da PDP keyi cewa idan dan takararsu bai ci zabe ba zasu tada rigima, sai tsohon shugaban yace dama irin wadannan maganganun na tasowa. Dalili ke nan da aka yi taron 'yan takaran inda Janaral Buhari daga APC da shugaba Jonathan daga PDP suka sa hannu a yarjejeniya suna neman a yi zaben lafiya. Yin hakan ya nunawa magoya bayansu cewa basa son rikici.

Janaral Babangida yace duk kasar da ake siyasa akwai maganganun tashin hankali na faruwa kuma babu wanda zai ce yaki yana da anfani. Ahalin yanzu, inji Janaral Babangida yana ganin kowa ya san anfanin zaman lafiya kuma babu yadda kasa zata ciga ba tare da zaman lafiya ba.

Duk wanda yayi imani cewa 'yan Najeriya basu da wata kasa da ta fita to ashe kuwa ba za'a yi abun da zai kawo wargajewarta ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG