‘Yan Nijeriya na cigaba da mai da martani game da dage zaben da aka yi. Mutum na faro da wakilinmu ya tuntuba ya ce, al’amarin na bukatar addu’a saboda mutane da yaw aba su ji dadi ba. Ya ce to amma haka Allah ya so; don haka kamata ya yi a rungumi kaddara a kuma yi addu’a Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi. Ya ce Allah ya sa hukumomin da abin ya shafa da shugabanni su yi adalci.
Mutum na biye kuwa cewa ya yi shure-shure baya hana mutuwa, kuma duk abin da ake gudan shi zai faru don masu iya magana sun ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Don haka muddun za a yi zaben to jama’a za su zabi abin da ya fi masu. Mutum na uku, wanda ya bayyana sunansa da Ahmed Modibbo Wali, kuma shi ne dan takarar gwamnan jam’iyyar APGA a jihar Gombe, ya ce sam ba su ji dadi ba saboda sun bata lokaci wajen yin kampe kawai sai aka ce wai an dage zabe da tsawon wata guda. To amma ya ce hakan bai sanyaya masu gwiwa ba, sai ma kwarin gwiwar da ya ba su.
Shi kuwa Kwamrad Garba Tela Yarwagana Wudil Gombe, PRO na jam’iyyar APC ya ce sam hakan bai masu dadi ba. To amma ya ce kar a daga hankali saboda alamu sun nuna cewa APC ke da nasara amma ake neman a yi kafar ungulu. Ya ce duk da haka dai daga karshe sai APC ta yi nasara. Ita kuwa wata mai suna Catherine Magaji cewa ta yi su masu biyayya ne ga gwamnati, don haka dayake dama ita ta ba da ranar 14 ga wata sannan ita din kuma ta dage zuwa 28. Hakan dai bai yi dadi ba, to amma su masu biyayya ne.