A yayin da aka kidaya kimanin kashi 70 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa a Saliyo, babbar jam'iyyar hamayya ta kasar ke kan gaba da 'yar karamar rata. Amma a yayin da aka fara ganin alamun cewa babu wata jam'iyyar da zata iya lashe zaben kai tsaye, 'yan takarar sun fara zawarcin wadanda zasu yi kawance da su idan har ta kama sai an gudamnar da zagaye na biyu na zaben fitar da gwani.
Dan takarar Jam'iyyar Sierra Leone Peoples Party(SLPP), Janar Julius Maada Bio,mai ritaya, yana da kashi 43.3 cikin 100 na kuri'un da aka kidaya, yayin da dan takarar jam'iyyar All Peoples Congress mai mulkin kasar, kuma tsohon ministan harkokin waje, Samura Kamara, yake da kashi 42.6 cikin 100.
Dan takara dai yana bukatar samun kashi 55 cikin 100 na adadin kuri;un da aka kada kafin ya lashe zaben a zagayen farko.
ZMUtane fiye da miliyan uku suka yi rajistar shiga zaben na ranar laraba, wanda yana daya daga cikin zabubbukan da aka fi rasa sanin gwani cikinsa a tarihin wannan kasa dake Afirka ta Yamma. Shugaban kasa mai barin gado Ernest Bai Koroma na jamiyyar APC zai sauka ne daga kan karagar mulkin bayan kammala wa'adin mulkinsa biyu.
Facebook Forum