Ministan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja Muhammad Bello ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan hare-haren da aka kai wasu kauyukan Abuja, da su ka yi sanadin mutuwar mutum guda da kuma kama wasu 10.
Ministan, wanda ke jaddada hakan ga ‘yan jarida bayan taron gaggawa jira Jumma’a da shugabannin al’ummomin da aka kai wa hare-haren, ya yi kira ga jama’a da a kai zuciya nesa dayake hukuma ta shiga al’amarin. Shi ma da yak e bayani ga wakilinmu, Kakakin Ministan Malam Abubakar Sani, y ace a Karamar Hukumar Kuje ne aka kai hare-haren kuma tuni Ministan y aba da jami’an tsaron umurnin tabbatar da tsaro ga jami’an tsaro; ya ce hadda a cikin birnin tarayyar Najeriya Abuja ma an dau matakan tsaro.
One Malam Shu’aibu Mungadi, an expert on the Capital Territory Abuja, y ace wata babbar mafita it ace kyautata ma bangaren tsaro rayuwa ta yadda bangaren shi kuma zai samu sukunin sa ido sosai kan miyagu ciki har da masu amfani da wayoyin salula don aika-aikarsu.
Ga wakilinmu a Abuja Hassan Maina Kaina da rahoton: