Wakiliyarmu ta Jos Zainab Babaji, wadda ta aiko da labarin, ta ruwaito daya daga cikin wadanda aka karrama a littafin wato tsohon babban kwamandan dakarun tabbatar da zaman lafiya na ECOMOG da aka tura kasar Saliyo, Janar Martin Luther Agwai, ya na cewa babu wani irin ikon hukuma ko soji da zai tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya in ba a daidaita wasu al’amura ba da su ka hada da kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da kuma siyasar ita kan ta.
Shi ma Gwamnan jihar Kaduna, ta bakin mai ba shi shawara ta bakin abubuwan da su ka shafi addinin Kirista, Rabaran John Joseph Hayab, ya ce kowani dan Nijeriya ma shugaba ne a irin matsayin da ya ke. Don haka, ya ce muddun ana so a gyara kasar sai kowa ya taka tasa rawar. Haka zalika, Sakataren darikar ECWA na kasa baki daya furfesa Samuel Kunyob y ace hakkin aiktata gaskiya ya rataya a wuyan kowa har da masinjan ofis.