Shugaban Hukumar Oyeyemi yace nan gaba kadan jami'an zasu fara rike makamai domin gudanar da ayyukansu na tabbatar da kiyaye haduran motoci.
Inji Mr. Oyeyemi daukan matakin ya zama wajibi idan aka yi la'akari da hadarorin da jami'an ke fuskanta.
Tuni jami'an kimanin dubu biyar suka samu horo akan yin anfani da makamai. Jami'an suna fuskantar matsaloli da direbobin motoci da ma wadanda ba direbobi ba.
Kwana kwanan nan wasu bata gari banza suka lakadawa wani jami'in hukumar duka a Legas. Irin wannan lamarin ne shugaban yace ba zasu amince dashi ba.
Saidai wasu direbobi na ganin bai dace jami'an su dinga rike makamai ba domin suna iya zama hadari garesu da fasinjoji.
Ga karin bayani.