Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Lauyoyi Sun Bukaci EFCC da ICPC Su Binciki Janar Dambazau da Janar Buratai


Janar Abdulrahman Dambazau, ministan tsaron cikin gida
Janar Abdulrahman Dambazau, ministan tsaron cikin gida

A Najeriya kafofin labarai sun dade sun bada rahotannin dake cewa Janar Buratai da Janar Dambazau sun mallaki wasu kadarori a kasashen waje ta hanyoyin da suke ganin bata dace ba.

Lauyoyin dake gwagwarmaya a Kano sun ce ya zama wajibi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su kaddamar da cikakken bincike akan wadannan manyan jami'an gwamnatin Buhari.

Ana zargin ministan alamuran cikin gida Janar Dambazau mai ritaya wanda shi ma tsohon babban hafsan mayakan Najeriya ne da mallakar kadarori a kasar Amurka. Shi ko Janar Buratai gidage biyu aka ce ya mallaka a Du Bai.

Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Barrister Audu Bulama Bukarti kakakin ayarin lauyoyin gwagwarmayar masu wannan yunkurin ganin an yi binciken kwakwaf akan manyan jami'an gwamnatin yace kafafen yada labarai sun yi rahotanni babban hafsan sojoji Janar Yusuf Tukur Buratai yana da gidaje biyu a Hadaddiyar Daular Larabawa, wato Du Bai.

Janar Buratai yace yana noman macizai, to amma ina gonar macizan take? Ya bayyanawa duniya nawa yake samu a matsayin riba. Idan kuma yana da wata hanyar samun kudi a fito a yi bayani dalla dalla. Inji Barrister Bukarti barin maganar kawai ba zai yiwu ba.

Yace shi ma Abdulrahaman Dambazau kafafen yada labarai sun fito da zarge zarge masu karfi a kansa. Yana da gidaje a waje. A Amurka kawai yana da gida na dalar Amurka miliyan uku ko kuma nera miliyan dubu daya da hamsin (N1050m). Kafofin yada labaran har ma da takardun ciniki sun buga. Sun buga sunayen kamfanonin da aka yi anfani dasu wajen sayen gidajen.

Lauyoyin sun ce idan adalci ake son yi to lallai ne binciken cin hanci da rashawa ya shafi manyan mutane idan an samesu da hannu dumu dumu cikin aikata halin muna muna. Kada a biniciki wasu a bar wasu.

Yace saboda haka suka rubuta wasika zuwa hukumomin EFCC da ICPC lallai su yi bincike na kwakwaf kan mutanen biyu.

Shi ma shugaban lardin arewacin Najeriya na kungiyar matasa masu kare martabar Buhari, Anas Abba Dala yace matakin lauyoyin ya yi daidai da abun da kungiyarsu ta sa a gabanta. Idan shugaba yana son kare mutuncinsa to ya zama wajibi a binciki mutanen idan ba haka ba kasar ba zata gyaru ba kuma za'a cigaba da tafiya cikin rashin adalci. Duk wanda aka sameshi da laifi a gurfanar dashi gaban kotu.

Idan hukumomin suka ki yin bincike Barrister Bukarti yace zasu garzaya kotu inda zasu gurfanar da hukumomin da mutanen.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG