Jami’yar APC a matakin jihohi ta fara jan hankalin gwamnati kan tayi hattara da irin mutanen da take basu mukamai don kaucewa matsaloli masu iya tasowa da zai shafi harkokin mulki a Najeriya.
Sakataren jami’yar APC a jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello yace rashin neman shawarar shugabannin jami’yar na jihohi kan wadanda gwamnati ke basu mukamai, zai iya zama illa ga harkokin gudanarwar gwamnati.Yace za'a samu damuwa sosai idan ba'ayi gyaraba. Saboda suna so a taimakawa talakawa, amma wadanda ake zabe basu tunanin talaka.
Shima sakataren APC a jihar Pilato, Bashir Musa Sati yace ba zasu kau da kai daga illar da suke hange wannan gwamnati zata fuskanta ba. Amma inda so samu ne, wadanda suka yi aiki lokacin zabe, sune yakamata anada.
A bangare guda kuwa ita gwamnati na cewa tana zaben wadanda suka chanchanta ne. A jawabinsa da yake nada kwamishinoni, Gwamnan jihar Filato, yace shi baya zaben wadanda suke kamun kafa.
A saurari cikakken rahoto daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Facebook Forum