Jami’an kiwon lafiya a fadin duniya na maida hankali wajan nazarin matakan da za a dauka don dakile yaduwar cutar Coronavirus, da ta kama akalla mutane dubu 82,000 a sama da kasashe 40, tun bayan lokacin da cutar ta bullo a China a karshen watan Disanban bara.
Amurka da Koriya ta Kudu sun dakatar da rawar dajin hadin gwiwa na sojojin da suke yi, kana Amurka ta fitar da wata sabuwar sanarwa inda ta ke ba ‘yan kasar shawara da su gujewa zuwa Koriya ta Kudu, kasar da aka fi samun wadanda suka kamu da cutar bayan China zuwa yanzu.
Ma’aikatan lafiyar Koriya ta Kudu sun fada yau Alhamis cewa akwai mutane 505 da suka kara kamuwa da coronavirus, abinda ya kara jimlar masu cutar zuwa dubu 1,766 a kasar.
Firaiministan Japan, Shinzo Abe ya bada umurnin rufe makarantu nan da wasu makonni, biyo bayan kiran da gwamnati ta yi ga mutane da su guji zuwa manyan taruka, da kuma shawarar da kungiyoyin ‘yan wasanni suka yanke kan ko dai soke wasannin ko kuma a yi wasan ba tare da yan kallo ba don a magance yaduwar kwayar cutar.
Akwai kusan mutane 200 a Japan da suka kamu da cutar, banda mutane sama da dari 700 da suka kamu da cutar a cikin wani jirgin ruwan shakatawa da aka killace tsawon makonni a tashar jirgin ruwa ta Yokohama.
A wani makamancin rahoto kuma, jiya Laraba shugaban Amurka Donald Trump ya ce baya tunanin ba za a iya kaucewa yaduwar annobar cutar Coronavirus a Amurka ba, cutar da ta kama sama da mutane dubu 80,000 a akalla kasashe 37, amma ya bayyana kwarin gwiwar cewa a shirye gwamnatinsa ta ke don daukar matakan da suka dace.
Shugaba Trump, a lokacin da yake magana da manema labarai a Fadar white House, ya kara da cewa hadarin kamuwa da cutar ga Amurkawa bai da yawa sosai.
Kalaman na Trump na zuwa ne kwana daya bayan da jami’ai daga hukumar da ke kula da dakile yaduwar cutuka ta Amurka da ake kira CDC a takaice ta bayyana cewa, tambaya daya da ake yi ita ce yaushe takamaimai kwayar cutar za ta bazu kuma mutane nawa ne a Amurka za su yi rashin lafiya mai tsanani.
Ya zuwa yanzu dai, adadin wadanda suka kamu da cutar a Amurka ya kai 60. Mutane uku daga cikin su sun je yankin Wuhan a China, inda cutar ta fara bulla, yayin da aka dawo da mutane 42 Amurka bayan da suka shiga wani jirgin ruwa, inda daruruwan mutane suka kamu da rashin lafiya yayin da aka killace jirgin a gabar tekun Japan.
Jami’an kiwon lafiya na nuna damuwa akan abin da suka kira yanayin kamu wa da cutar ba tare da mutum ya san yadda ya kamu da cutar ba, abinda ake kira “Community spread” da turanci.
Facebook Forum