Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijer ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Batun Yada Labaran Karya


Le président nigérien Mohamed Bazoum lors d'une conférence de presse à la Chancellerie de Berlin, le 8 juillet 2021.
Le président nigérien Mohamed Bazoum lors d'une conférence de presse à la Chancellerie de Berlin, le 8 juillet 2021.

A jamhuriyar Nijer Hukumar sadarwa wato CSC ta gargadi kafafen yadada labarai akan maganar mutunta ka’idodin aiki don gujewa haddasa rudani a kawunan al’uma a irin wannan lokaci na fama da matsalar tsaro. Hukumar na tunatarwa game mahimmancin aikin tantance sahihanci labari kafin a yada don kauce wa cin zarafin wasu sai dai kungiyoyin ‘yan jarida na ganin akwai alamun wuce makadi da rawa a kiraye kirayen na CSC.

A sanarwar da ta fitar a game da yanayin da kafafen labarai ke gudanar da ayyukansu a hlin yanzu a Nijer, hukumar sadarawa ta CSC ta ce lura da yadda wasu suka dukufa wajen bada labarin kanzon kurege a maimakon gudanar da bincike domin tantance gaskiyar labari ba, misalin wani labrin da jaridar Canard en furie ta ruwaito a wannan mako game da wasu kudade sama da biliion 9 da ta ce an ware wa matan shuwagabanin kolin kasar nan domin su kashe wutar gabansu, wato fonds ploitique. Dr Sani Kabir shugabn hukumar sadarwa ta CSC, ya yi Karin bayani ga Muryar Amurka.

Ko akan matsalar tsaron da ake fama da ita a Nijer ma kafafe da dama na kauce wa ka’idar yadda ake bada irin wannan labari, inji Dr Sani Kabir .

Koda yake ya yarda cewa akwai kamshin gaskiya a abubuwan da hukumar ta CSC ke kashedi akansu, Sakataren Yada Labarai na gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida Maison de la presse, Souleymane Oumarou Brah na ganin alamun wuce gona da iri a wannan yunkuri.

Hukumar ta lashi takobin buga sanda akan duk kafar da aka samu da laifin baza karya ko yi wa wani Kazafi da kuma wadanda ke neman tunzura jama’a a fannin tsaro.

Saurari rahoton Souleyman Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG