Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Na Zaman Makokin Mutuwar Sojojinta Fiye Da 70


Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015
Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015

Majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Nijar ta bukaci kasashen duniya su taimakawa takwarorinsu na yankin Sahel a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta soma zaman makokin kwanaki 3 daga yau juma’a a, da nufin nuna alhinin rasuwar sojojinta sama da 70 sakamakon harin ta’addanci da aka kai a barikin Inates,

A sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a yammacin jiya Alhamis ‘yan adawa da masu rinjaye a majalisar dokokin sun fara ne da jajantawa ‘yan kasa a game da wannan babban rashi.

‘Yan majalisar sun kuma jinjinawa dakarun da suka kwanta dama a yayinda suke kokarin kare martabar Nijer da jama’arta.

La’akari da hanyoyin da ‘yan ta’adda ke amfani da su a hare haren da suka kai a ‘yan makwanin nan a kasashen Mali Burkina Faso da jamhuriyar Nijer ya sa majalisar jan hankulan kasashen duniya su farka daga barci..

Gwamnatin jamhuriyar Nijer a cewar kakakinta Zakaria Abdourahamane, ta ware kwanaki 3 na zaman makoki daga yau juma’a da nufin nuna alhinin wannan rashi sannan ta bukaci kowane dan kasa ya ware minitoci 5 daga karfe 10 na safiyar yau domin yin addu’oi ga sojojin da suka rasu akan aikin tabbatar da tsaron kasa..

Da hantsin wannan juma’a ne za a yi jana’izar sojoji 71 din nan da suka kwanta dama a yayin gumurzun da suka yi da ‘yan ta’adda da suka kai hari a barikin sojan Inates kan iyakar Nijer da Mali a ranar talatar da ta gabata.

Kasashen duniya na ci gaba da aikewa da sakwannin ta’aziya ga kasar ta Nijar.

Jakadan Amurka a Nijer Eric P. Whitaker ya bayyana cewa kasarsa ta yi matukar kaduwa da faruwar wannan al’amari sai dai Amurka ba zata taba gajiya ba wajen tallafawa Nijer a yakin da ta kaddamar da yaki da ta’addanci.

Ga karin bayani daga Souley Moumouni Barma

Zaman makokin mutuwar sojoji a Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG