Ita dai wannan matsalar ruwa a Damagaram ba sabon abu ba ne.
A ko wace shekara a daidai wannan lokaci a kan fuskanci karancin ruwa, alhali lokaci ne da aka fi bukatar ruwan, jama'a sun koka na wahalar da suke sha wajen neman ruwa yayin da wasu ke yin tafiya mai nisa , wasu su kwana a pompo, wasu ma sun ce sanadiyar haka azumin ma sukan ajiye shi.
Kampanin gidan ruwa SEEN da ke da nauyin wadata jahar Damagaram da ruwan sha ta ta'allka matsalar da rishin katfin wutar lantarki da ake fuskanta a 'yan kwanakin nan, inda daraktan kampanin Illiya Mayau ya ce suna nan da hukumomin jihar sun hadu don samu mafita, inda ya ce sun yi tsari na rarraba ruwa a unguwanni baki baki kafin a shawo kan matsalar.
Shi ma daga na shi bangaren kampanin gidan wuta wato NIGELEC ta bakin daraktan Riba Gado ya ce rage karfin da ake samu na wutar lantaki a kwanakin nan yana da nasaba da cibiyarsu daga bangaren Najeriya a yadda suke tsammani, amma ya ce tuni ma'aikatan su da ma na Nigeriya sun dukufa wajen samo bakin zaren.
Sai dai a kullum jama'a na mamakin yadda ko yaushe masu neman mulki na fakewa da matsalar ruwan don yi musu alkawura, wanda har yanzu suke ganin bai cika ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: