Alhaji Danjuma Khali daraktan kungiyar agaji a jihar Filato yace 'yan agaji da 'yan sintiri idan abu ya faru sukan bada agaji cikin gaggawa. Sabili da haka yace ya zama wajibi a basu fadakarwa akan yadda zasu gudanar da ayyukansu da kuma yadda zasu kare kansu. Sun kuduri aniyar shirya irin wannan horon a duk fadin kasar da zai kunshi Musulmi da Kirista. Yace Najeriya kasarsu ce domin haka dole Musulmi da Kirista su zauna tare. Babu wanda zai kori wani. Hadin kai shi ne maganin rabuwar kai.
Manjo Aminu Uba shi ya wakilci kwamandan rundunar tsaro. Yace aikin tsaro ba na 'yansanda ko na sojoji ba ne kawai. Kowa jami'in tsaro ne. Duk inda aka ga mutumin da ba'a gane ba ko wani abu da ba'a gane ba to a kira jami'an tsaro. Idan an ajiye jaka ko mota har na wani lokaci to kamata yayi a kira jam'an tsaro.
Ga cikakken rahoton Zainab Babaji.