Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Gombe ta bayyana dan takarar Jam’iyar APC, Muhammed Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a ranan Asabar din da ta gabata.
Jami’in tattara sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Gombe da na 'yan majalisar dokoki, Farfesa Saminu Abdulrahman Ibrahim, ya ce dan takarar APC, Yahaya, ya lashe da kuri’u 364,177, yayin da Sanata Usman Bayero na jam’iyyar PDP ya zo na biyu.
Magoya bayan jam’iyyar APC sun yi ta kade-kade da wake-wake don bayyana murnansu a sassan jihar.
A jihar Bauchi da ke makwabataka da Gombe, akasi aka samu, domin jami’in tattara sakamakon zabe a jihar, Farfesa Muhammed Kyari, ya ba da umurnin soke zaben da ya gudana a karamar hukumar Tafawa Balewa saboda soke ya ce a sake sabon zabe nan da kwanaki 21.
An ayyana zaben na Bauchi a matsayin wanda ba a kammala ba, saboda 'yan tashe-tashen hankula da aka samu, sannan adadin kuri'un da aka soke a tsakanin jami'iyyun da ke takara, sun wuce adadin da doka ta tanada.
Sakamakon zabubbukan da aka amince da su a yankunan kananan hukumomi 19 na nuni da cewa jam’iyyar PDP ce take da mafi yawan kuri’u dubu 469, 512, sai mai bin ta jam’iyyar APC mai mulki da kuri'u 465,453.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi: