Jam’iyyar demokarats a Amurka ta nuna alamun fargaba game da annobar coronavirus wacce ke kara yaduwa, yayin da ta yanke shawarar gudanar da wani taro ta kafar yanar gizo inda za a nada tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, sabanin yadda ta saba gudanar da taron gaban dumbin jama’a.
Kwamitin da ke sanya ido kan dokokin jam’iyyar ya amince ranar Talata cewa zai bai wa wadanda zasu shirya taron damar shirya shi yadda ya kamata. Za a fara taron ne ranar 17 ga watan Augusta, a cikin wani filin buga kwallon Kwando da ke jihar Wisconsin.
Kafin a samu bullar coronavirus, da jam'iyyar Demokarat da Republican sun saba gudanar da wannan taron na tsai da dan takarar Shugaban kasa bayan kowane shekara hudu, inda akan ga mutane wajen 50,000 a biranen da ake gudanar da taron, ciki har da wakilan 'dalaget' da kuma 'yan jarida wajen 20,000.
Facebook Forum