An kira wani taron gaggawa na musamman na wata majalisar gaggawa ta gwamnati jiya laraba a bayan wannan harin.
Firayim minista Cameron ya bayyana kashe mutumin a zaman abin kyama, yana mai cewa dukkan alamu sun nuna cewa harin ta’addanci ne. Sashen yaki da ta’addanci na rundunar ‘yan sandan Scotland Yard yana jagorancin wannan bincike, amma babu wani bayani mai yawa da aka samu daga hannun hukuma.
‘Yan sanda sun harbe suka raunata maharan su biyu wadanda a yanzu haka suke wani asibiti ana gadinsu. An yi imanin cewa mutumin da suka kashe sojan Britaniya ne, amma har yanzu ba a bayyana ko shi wanene ba.
Shaidu da suka ga wannan lamarin sun ce a bisa dukkan alamu, mutanen biyu da ake zargi sun yi ta sarar mutumin ne da wukake irin na fawa, inda aka ga jini ko ta ina a gefen hanya inda lamarin ya abku.
Gidan telebijin na Britaniya ya watsa bidiyon da wani shaida a wurin ya dauka na wani mutumi duk hannunsa jini yana rike da wuka da kuma karamar adda. A ciki, an ji mutumin yana cewa “ba zaku taba zama cikin tsaro ba, in kun cire mana ido mu cire naku, in kun cire mana hakori, mu cire muku hakori.”
Ya nemi gafarar cewa akwai mata da yara kanana a wurin wadanda suka ga yadda aka kashe mutumin, amma ya ce, “a kasarmu, ala tilas mata su na ganin irin wanna.” Bai fadi ko wace kasa yake nufi ba. ‘yan jarida na Britaniya sun ce turancinsa na kama sosai da irin lafazin mutanen birnin London.
Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka yayi tur da harin yana mai fadin cewa Amurka tana bayan kawarta Britaniya daram a irin wannan tashin hankali na rashin kan gado.
A cikin hira da ya yi da Salihu Garba, Wakilin Sashen Hausa a birnin London Sani Dauda ya bayyana yadda lamarin ya auku.