Sakamakon farkoj na kuri’ar raba-gardama da aka kada a kasar Ireland, ya nuna cewa al’umar kasar, sun amince da a halalta auren jinsi daya.
Nan gaba a yau ne ake sa ran za a fitar da sakamakon karshe bayan da bayanai ke nuna cewa wadanda suka amince da auren na jinsi guda sun fi yawa.
Wannan dai shi ne karo na farko a duk fadin duniya da aka taba gudanar da irin wannan kuri’a kan auren jinsi daya a kasar da ke bin mazhabar Katolika.
Wannan matsaya da ‘yan kasar suka dauka, na zuwa ne shekaru kusan 20 bayan da aka cire luwadi a matsayin laifi.
Rahotanni na cewa dubban ‘yan kasar ta Ireland mazauna wasu kasashe, sun yi tattaki zuwa gida domin kada kuri’unsu.
Yanzu haka a nahiyar Turai, an halalta auren jinsi guda a fiye da kasashe goma, an kuma yi irin hakan ma a kasashen Brazil, da Argentina da Canada da New Zeland da Afrika ta Kudu da kuma wasu jihohin Amurka.