Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Ta Tsinci Gawarwakin Wasu Daga Cikin Mutanenta Da Aka Yi Garkuwa Da Su


Dakarun Isra'ila. (Photo by JACK GUEZ / AFP)
Dakarun Isra'ila. (Photo by JACK GUEZ / AFP)

A halin da ake ciki, Isra'ila na kokarin yi wa birnin Rafah kawanya, suna masu cewa birnin shi ne mabuya ta karshe ga mayakan Hamas.

Dakarun Isra’ila sun gano gawarwakin wasu mutane uku daga cikin 'yan kasarta da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Sojojin kasar sun fada a ranar Juma’a cewa tun a harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin Isra’ila aka kashe mutanen.

Sai dai sojojin ba su fadi takamaiman inda suka gano gawarwakin a yankin na Gaza ba.

Dakarun Isra’ila a halin da ake ciki na kokarin yi wa birnin Rafah kawanya, suna masu cewa birnin shi ne mabuya ta karshe ga mayakan Hamas.

Sun kara da cewa anan kuma ake garkuwa da sauran Isra’ilawan da aka kama.

Akalla Isra’ilawa 1,200 suka mutu a ranar harin na 7 ga watan Oktoban bara, mafi aksarinsu fararen hula.

Sannan Hamas ta yi garkuwa da mutum kusan 250, sai dai kusan rabinsu an sako su a lokacin da aka cimma matsayar dakatar da bude wuta a watan Nuwamba.

A hare-haren martanin da Isra’ila ta kai tun daga lokacin sun halaka Falasadinawa sama da dubu 35.

Isra’ila ta ce har yanzu akwai kusan mutum 100 a hannun Hamas da kuma gawarwakin sama da mutum 30.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG