Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Islam Bai Yarda da Haka ba


(File Photo)
(File Photo)

An yi kira ga 'yan boko haram dasu sako 'yan matan da suke garkuwa dasu.

Daurruwan mata musulmai sunyi gangami a birnin Yamai domin numa bakin cikinsu bisa sace ‘yan mata na makarantar garin Chibok a arewacin Najeriya.

Kungiyar sun kuma yi kira ga ‘yan Boko Haram dasu sako ‘yan matan da sukayi karkuwa dasu a dajin yau wata daya kennan.

Kungiyar, na mata musulumin jamhiriyar Nijer sun nuna alhininsu kan yanda rayuwa ‘yan matan ke ciki biyo bayan daukesu da kungiyar Boko Haram tace tayi daga makaranta.

Kakakin kungiyar matan malama Hudat, tana mai cewa “muna kira da sunan Kur'ani da darajan shi,da sunan Rahama Muhammad sallalahu alaihim wasalam su maida wadannan matan gidajensu,in akwai wani abu tsakaninsu da gwamnati to suyi kayansu amma wadannan ‘yan mata su dawo dasu domin Islam bai gayama haka ba.”

Matan sun yaba da kokarin da kasashen duniya sukeyi domin ganin su ceto ‘yan matan na gari Chibok da fatan haka zata cima ruwa.
Islam Bai Yarda da Haka ba - 2'29"
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG