Suna daga cikin sama da mutane ishirin da aka kama dangane da yajin aikin da aka gudanar a yankunan kasar Kamaru da ake amfani da harshen ingilishi. Kira da ake yi na neman sakinsu yana kara haifar da tashin hankali, ya kuma kasance kadangaren bakin tulu a zaman tattaunawa, yayin da yajin aikin ya shiga wata na bakwai.
Mutane 27 da aka kama dangane da yajin aikin sun sake bayyana gaban kotun sojin ranar Laraba.
Ranar talatin ga watan Mayu, alkalin kotun kanar Abega Mbezoa Eko Eko yace shugabannin biyu da aka kama lauya Felix Nkongbo Agbor Balla da Fontem Neba, za a basu abin da ya kira takaitaccen ‘yanci, sai dai ba a bada belinsu ba ranar laraba a zaman na kotu.
Masu shigar da kara sun bada hujjar cewa, mutanen da ake tuhuma da abin da ake dangantawa da ta’addanci da ake iya yankewa hukumcin kisa, bai kamata a bada belinsu ba.
Facebook Forum