Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Bukaci Amurka Ta Daina Mata Barazana


A 'yan kwanakin nan dai ana ta tada jijiyar wuya tsakanin Amurka da Iran, ta yadda Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi kira ga Amurka da ta bi hanyar mutuntawa a mai makon yi mata barazana.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammed Javad Zarif, ya yi kira ga shugaban Amurka, Donald Trump, da ya bi hanyar “mutunci” a maimakon ya rika amfani da barazana.

Zarif na maida martani ne dangane da wani sakon Twitter da Trump ya wallafa a jiya Lahadi inda yake cewa “idan Iran tana so ta yi fada ne, wannan zai kasance karshenta a hukumance. Kul! ta sake barazana ga Amurka.

Ministan ya kara da cewa, Trump, yana fuskantar matsin lamba ne daga wani rukunin mutane, ciki har da mai ba shi shawar kan harkar tsaro, John Bolton, da kuma Firaiminstan Isra’ila, Benyamin Netanyahu, inda ya ce, yana kuma so ne ya cimma wani abu da magabatansa suka gaza yi.

Zarif ya kuma rubuta cewa, “Iran ta kwashe shekaru aru-aru tana nan daram, yayin da masu musguna mata duk suka durkushe, matakan ta’addanci da aka dauka kan tattalin arzikinmu da surutai marasa kan gado, ba za su kawo karshen Iran ba.”

A makon daya gabata, Trump ya nuna alamun janyewa daga zafafan kalaman da yake yi akan Iran, inda ya nuna cewa a shirye yake a yi zaman tattaunawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG