Kasar Iran ta bayar da sammacin kama shugaban Amurka Donald Trump da wasu mutane 35, bisa laifin kashe janar Qassem Soleimani.
Babban mai shigar da kara a Tehran Ali Alqasimehr ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Fars.
Amurka ta kashe Soleimani, kwamandan runduna ta musamman ta juyin juya hali, a wani harin jirgin sama maras matuki a ranar 3 ga watan Janairu.
Amurkar ta zargi Soleimani da hannu a kitsa wasu hare-hare kan wasu dakarun sojinta da ke Iran.
Alqasimehr ya ce an bayar da sammacin ne bisa tuhumar laifukan kisa da kuma ta'addanci. Ya ce Iran ta bukaci rundunar 'yan sandan kasa-da-kasa ta "INTERPOL" da ta sanya alamar gargadi kan Trump da dukkanin sauran mutanen da ake zargi da wadannan laifukan.
Duk da dai bai bayar da sunayen sauran mutanen ba, amma Alqasimehrya ce sun hada jami'an sojin Amurka da kuma wasu jami'an fararen hula.
"Iran za ta ci gaba da bibiyar wannan batu bayan Trump ya sauka daga mulki," a cewar Alqasimehr.
Kisan Soleimani ya janyo zaman dar-dar a tsakanin Amurka da Iran bayan da Iran ta mayar da martani tare da harba makamai masu linzami kan wasu sansanonin dakarun Amurka da ke Iraqi.
Facebook Forum