LEGOS, NIGERIA - A shirin Ilimi na wannan makon, mun duba yadda ake nuna wariya da ake yi wa daliban da suka kammala karatun kimiyyar kere-kere a aikin Gwamnati a Najeriya, hukumar kula da fasahar kere-kere ta kasa ta kaddamar da wani shiri na shekara daya ta yanar gizo ga masu rike da manyan difloma na kasa da su canza shedarsu zuwa digiri na farko.
A wata hira da Babban Sakataren Hukumar Farfesa Idris Bugaje da sauran dalibai za a yi wannan shirin ne ta yanar gizo tare da jami’o’in kasashen waje da aka amince da su.
Saurari cikakken shirin da Babangida Jibrin ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna