Da yake magana a lokacin bita ta musamman da sanannun malaman addinin Islama suka yi ma junansu a kan yaki da cutar Polio a bayan da suka komo daga wani taron malaman kan wannan batu a kasashen larabawa, Ustaz Hussaini Zakariya ya ce, "...duk wani malamin da ya yaudari mutane...(da)nufin cutar da su, to ba ya ha'inci mutane ba ne, ba ya yaudare su ba ne...Hukumcinsa sai Allah Subhanahu Wa Ta'ala domin ya hallakar da mutane, ya nakkasar da su, ta abinda yake ba haka din ba ne...."
Sanannen mai wa'azin na Islama, yace ba zai yiwu a ce a duk duniya babu wani wanda yake da ilmin cewa akwai cuta a cikin maganin rigakafin Polio ba sai mutum daya, ko kuma wasu 'yan tairarrun mutane wadanda yake a kasarsu ba a yin wannan magani, ba su cikin wadanda suka kirkiri wannan magani, alhali jama'a a ko ina a duniya sun amfana da wannan maganin ta hanyoyi dabam-dabam.
Ustaz hussaini Zakariya yace babu wani abinda zai sa al'ummar Musulmi na Najeriya su kara komawa baya cikin duhun daji, su koma cikin jahilci, su zama koma-baya a cikin al'umma kamar a ce a yau Musulmin ne kadai, kuma na Najeriya tak, suka rage a baya a wannan ciwo da ya addabi 'ya'yanmu gaba daya.