Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta ce Ta Sami Gagarumar Nasara a Yakin Da Take Yi Da ‘Yan Ta'adda A Sokoto


Rundunar Sojojin Najeriya
Rundunar Sojojin Najeriya

A daidai lokacin da Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta sami gagarumar nasarori a yakin da take yi da ‘yan ta'adda a yankin gabashin jihar Sokoto, mazauna yankunan sun ce har yanzu ba za'a rasa fargaba ba, domin ‘yan bindigar suna nan kusa da jama'ar yankin.

Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air marshall Sadiq Baba Abubakar shi ne ya furta batun samun nasarar a wurin bikin da rundunar sojin sama da ke jihar Sokoton ta gudanar don taya murnar Sallah ga sojojin da ke bakin daga a yankin.

Air marshall Sadiq Baba Abubakar, ta bakin kwamandan rundunar dabarun kai farmaki da jirage, AVM Olusegun Philip ya ce, aikin da mayakan saman suke gudanar wa ya taikamaka gaya wajen dakile ayukan ta’addanci a yankunan.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, sun gudanar da bikin sallah lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba. Amma sun nuna damuwarsu da fargaba, domin a cewar su ‘yan bindigar suna kusa da yankunan nasu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG