Hukumomi a kasar Madagascar na shirin aika sojoji da jami’an kiwon lafiya birnin Toamasina, birni na biyu mafi girma a kasar, don dakile yaduwar annobar COVID-19.
Tun daga ranar Alhamis an sami karuwar mutum 122 da ke dauke da cutar. Sojojin da za a aika za su gudanar da aiki na tabbatar da zaman lafiya da ganin jama’a sun kiyaye doka wajen saka takunkumin rufe fuska da ba da tazara.
Mai Magana da yawun kwamitin yaki da annobar COVID-19 ya ce likitoci za su gudanar da bincike akan ko mace-mace da aka samu a bakin tekun Indiya na da alaka da annobar Coronavirus, ko kuma wata cuta ce daban.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da ganin wasu gawarwaki akan titin birnin na Toamasina, wanda ba a san musabbabin mutuwarsu ba.
AFP ta ce ministan sadarwar kasar, Lalatiana Rakotondrazafy, ya karyata samun wasu gawarwaki akan titi, amma kuma an tura wasu jami’ai zuwa birnin na Toamasina a dalilin barkewar cutar ta COVID-19.
Madagascar ta tabbatar da mutum 527 dake dauke da cutar a kasar inda mutum biyu ne kawai suka mutu sakamakon cutar.
Facebook Forum