Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyya mai mulki, Evariste Ndayishimiye ya ci zaben Shugaban kasar Burundi da gagarumin rinjaye bisa ga sakamakon wucin gading da aka fitar.
Sai dai babbar jam’iyyar adawa na ikrarın cewa an tafka magudi.
Hukumar zabe mai zaman kanta (CENI) ta bayyana abin da ya samu na sakamakon zaben zuwa jiya Litini, mai nuna cewa Ndayishimiye ya samu kashi 69% na kuri’un da aka kada, sannan shi kuma babban mai ja da shi Agathon Rwasa na jam’iyyar adawa ta CNL ya samu kashi 24% na kuri’un.
Mataimakin Shugaban kasa na daya Gaston Sindimwo na jam’iyyar ‘yan kishin kasa ta Uprona, ya tashi da kashi 2% kawai.
Nan da nan jam’iyyar CNL ta fara kokawa inda mai magana da yawun jam’iyyar Terence Manirambona ya fadawa Sashen Yankin Tsakiyar Afuika na Muryar Amurka cewa, CNL na da alkaluman da su a tabbatar cewa Rwasa ne ya ci zaben.
Facebook Forum