AGADEZ, NIGER - Tuni kuma hukumomi suka dauki matakin hana yaduwar cutar ta hanyar bada magani kyauta ga duk wanda aka ga alamun cutar a tattare dashi.
A halin da ake ciki yanzu an tabbatar da mutane 70 da suka kamu da cutar ta mashako a kananan hukumomi 13 dake arewacin kasar inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutun bakwai.
Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar yara ne da kuma tsofaffin jihar Agadas, wanda na daga cikin jihohin Nijar da cutar tafi kamari inda tuni hukumomin kiwon lafiya suka dauki dukkan matakan dakile bazuwarta ta hanyar bada maganin rigakafin cutar a yankunan da aka samu bullarta.
An kuma kafa kwamiti dake tattauanawa kan yadda za’a shawo kan cutar inda aka kafa wani tsari na yiwa mutane gwaji domin gano cutar inji Shugaban Kananan Asibitoci a Agadas, Dr. Yusha’u
Hukumomin dai sun ce ta hanyar wayar da kan al’umma wajen zuwa asibitoci ne zai a iya magance, ba ma cutar ta mashako ba kadai, har ma da wasu cututukan.
Hukumomin kiwon lafiya a Nijar sun bukaci jama’a da su sanya ido sosai tare da kai rahoton duk wanda aka ga alamun cutar a tattare da shi domin daukar matakin da ya dace na gaggawa.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna