Majalisar dokokin Turkiya ta amincewa gwamnatin kasar tayi anfani da karfin soji a Syria da Iraki akan ‘yan kungiyar ISIS. Wannan amincewar ta ba gwamnatin dama ta yaki mayakan Daular Islama da yanzu suna kusa da iyakar kasar.
Dokar da suka kafa ta kuma ba kasashen waje damar yin anfani da kasar Turkiya wajen kai hari akan ‘yan kungiyar ISIS.
Amurka tana jagorantar kawancen kasashe da suke hamayya da mamayar yankuna da kungiyar keyi. Wakilin Amurka Janaral John Allen wanda yake shugabancin hamayya da kungiyar ta ISIS zai tafi Turkiya a cigaba da rangadin da ya kai yankin da ya soma jiya Alhamis da kasar Iraki.
An samu matsi cikin ‘yan makonnin nan a kasar Turkiya yayin da mayakan ISIS ke kara kutsawa cikin yankunan Kurdawa da suke Kobani , garin dake kan iyaka da Turkiya. Ana kuma kiran garin Ayn al-Arab.
Babban jami’in tsaro dake garin da ‘yan kungiyar ke yiwa barazana a bangaren Syria dake kudancin iyaka da Turkiya ya gayawa Muryar Amurka cewa kungiyar zata yi kisan kare dangi idan kasashen duniya basu kawo doki ba.