Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dino Melaye Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Hannun 'Yan Sanda


Dino Melaye
Dino Melaye

Wata hatsaniya ta barke yayin da wasu 'yan daba suka kwace Sanata Dino Melaye daga hannun 'yan sandan SARS a Area 1 da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito a shafinta na yanar gizo cewa wasu motocin Hilux guda biyu ne suka sha gaban motar 'yan sanda da ke dauke da sanatan.

Yanzu dai rohotanni na nuna cewa Sanatan na wani asibiti da ake kira Zankili Medical Center a unguwar Mabuchi da ke birnin na Abuja domin samun kulawa saboda raunin da ya samu a yunkurin kubutar da shi da aka yi daga hannun 'yan sanda, a cewar jaridar Cable.

A jiya Litinin ne aka tsare Sanata Dino Melaye a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe wanda daga baya aka sakeshi amma sai 'yan sanda suka yi masa diran mikiya a gidansa da ke Abuja har sai da ya mika kansa ga 'yan sanda da safiyar Talata.

A baya dai 'Yan sanda na zargin Melaye da kin bayyana a gaban kotu don fuskantar shari'a a bisa zargin da ake masa na daukar nauyin wasu bata-gari da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Sauran bayani na nan tafe...

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG