Haka ma hukumar zata yi wa masu kada zabe ragista kana ta fadada mazabu kamar yadda mataimakin darektanta mai hulda da jama'a Nick Dazan ya yi karin haske. Ya ce akwai wadanda ba'a yi masu adalci ba. Wasu mazabu na da girma da yawan jama'a wasu kuma kanana ne amma an basu matsayi daya. Abun da hukumar zata yi shi ne ta tabbatar da cewa duk mazabun sun zama daya, babu wanda ya fi wani a girma da jama'a. Wuraren da mutane suka kaura za'a yi masu kwaskwarima kafin zaben 2015
Amma duk wani kwaskwarima da hukumar zata yi zai samu karbuwa ne idan da hannun jam'iyyu kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar CPC Mustafa Salihu ya fada. Ya ce jam'iyyun zasu zauna da hukumar su yadda da abubuwan da za'a yi kafin a aiwatar da su.
Da can baya hukumar ta yi anfani da masu zurfin ilimi kamar su shehunan malaman jami'o'i domin aiwatar da bayyana sakamakon zabe.
Nasiru El-Hikaya na da rahoto.