Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Kusan 50 a Wani Hari a Afghanistan


Tarkacen takalma da tufafin wadanda harin ya rutsa da su.
Tarkacen takalma da tufafin wadanda harin ya rutsa da su.

A cigaba da zubar da jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba da aka yi a Afghanistan, wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane wajen 50.

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa cibiyar raba katunan masu zabe a Kabul babban birnin Afghanitan da safiyar yau din nan Lahadi, ya hallaka mutane a kalla 48 ya kuma raunata wasu 100.

Mai magana da yawun Ma’aikatan Cikin Gida Najib Danish ya gaya wa Muryar Amurka cewa mutane na jira a waje a kan layin karbar katin zabe (ko Tazkira) don su samu izinin zabe yayin da maharin ya tayar da bama-baman da ya yi jigida da su.

Majiyoyin asibiti sun ce akalla 10 daga cikin wadan da su ka ji raunuka na cikin mawuyacin hali.

Tuni kungiyar ISIS ta dau alhakin kai harin.

Babban mukaddamin Afghanistan Abdullah Abdullah ya yi Allah wadai da abin da ya kira “harin ta’addanci” wanda aka kai kan cibiyar da aka kafa a wata makarantar da ke birnin Kabul.

“Ina tare da wadanda wannan aika-aika ta gaulaye ya shafa. Za mu cigaba da kudurinmu na tabbatar da gudanar da sahihin zabe kuma sam ‘yan ta’adda ba za su yi nasarar hana abin da mutanen Afghanistan su ke so ba,” a cewar Abdullah ta kafar twitter.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG